Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Buhari a London

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wadan su gwamnonin kasar guda bakwai a yau da yamma a Abuja House dake birnin London wanda cikin har da dan jam’iyyar PDP.

Ziyarar ta yau ta biyo bayan wata ziyara da wadansu gwamnonin suka kai a satin daya gabata wadanda suka hada da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmed El-Rufai.

Gwamnonin na yau sun hada da Abdullahi Umar Gwanduje na jihar Kano, Tanko Al-Makura na jihar Nassarawa, Samuel Ortom na jihar Benue, Kashim Shettima na jihar Borno, Dave Umahi na jihar Ebonyi da Abdulaziz Yari na jihar Zamfara sai kuma Abiola Ajumobi na jihar Oyo.

3089total visits,9visits today


Karanta:  Shugaba Buhari ya gana da sarakunan gargajiya

Leave a Reply

Your email address will not be published.