Gyaran Kundun Tsarin Mulki: Majalisar Wakilai ta amince da rage shakarun takara

Majalisar Walikai ta Najeriya ta amince da kudurin rage shekarun ‘yan takarkaru wadanda suka shafi matakan majalisun kasar da kuma shugaban kasa.

Majalisar ta amince da ragin shekarun shiga zabe na matakin Shugaban Kasa da ‘Yan Majalisun Dattijai da Wakilai wanda bayan kada kuri’a da akayi kudurin ya sami amincewar ‘yan majalisu 261 da kuma 23 wadanda suka ki amincewa da kudurin.

A wani bangaren kuma majalisar ta amince da kudurin da ya nemi a bawa mata kashi 35 a cikin kaso 100 na mukaman ministocin kasar wanda shima ya sami amincewar ‘yan majalisu 248 gami da kin amincewar 46. Sai kuma bangaren bawa kananan hukumomin kasar cin gashi kai wanda shima ya samu amincewar ‘yan majalisu 291 da kuma 12 wadanda suka ki amincewa.

Bugu da kari majalisar ta amince da kudurin sanya tsofaffin shugabannin majalisar dattijai da wakilai cikin taron sati-sati na kasar wanda ake kira da Members of the Council.

A baya bayan nan ne dai kungiyoyi da dama sukayi ta kiranye akan tabbatar da amincewar majalisar kan kudurin rage shekarun ‘yan takararkaru domin bawa samari matasa damar shiga zabe a kasar.

2701total visits,2visits today


Karanta:  'Yan majalisar Nigeria sun sayi motocin 'kece-raini' 200

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.