Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood

Jarumar ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ta fara gwada sa’arta a fina-finan Nollywood ne domin ta gwada basirar da take da ita ta yin fina-finai a bangarorin daban-daban.

A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.

“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’ Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim”Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim”

6502total visits,12visits today


Karanta:  'Dan autan' mawakan hip hop na Hausa Lil Ameer ya rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published.