Hadiza Gabon ta ziyarci Kasa Mai Tsarki

Jaruma Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta samu ziyartar Kasa Mai Tsarki wato Saudi Arabia a cikin satin da ya gabata inda take aiwatar da aikin Umara.

Jarumar wadda ta wallafa hoton ta a garin Madina sanye da bakin hijabi a shafukan ta na sada zumunta da suka hada sa Instagram da Facebook  mai dauke da taken “The past is a place of reference, not a place of residence” a ranar Alhamis data gabata ta samu sauka a garin na Madina a wannan rana ta 8 ga watan Nuwanba na 2018.

Sai dai tun wannan rana Jarumar bata sake wallafa wani abu ba dangane da tafiyar ta ta.

87total visits,87visits today


Karanta:  Na fi son shinkafa da mai da yaji - Hadiza Gabon

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.