Tarihin Hadiza Aliyu Gabon

Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da suna “Hadiza Gabon” wata Jaruma ce a masana’antar fina finan Hausa ta Kannywood a Najeriya. An haifi Jaruma Hadiza Gabon a ranar 1 da watan Yuni na shekara ta alif dari tara da tamanin da tara (1 June 1989) a garin Libreville na kasar Gabon.

Yawa yawan mutane a cikin masana’antar Kannywood da ma wajen ta baki daya kan kalli Hadiza Gabon a matsayin “Sarauniyar Mata”. Ta kasance mace mai kamun kai a masana’antar gami da girmama na gaba da ita. Bugu da kari ba’a taba samun ta da wani ashararanci ba irin wanda akan zargi fitattun Jarumai mata da shi.

Hadiza kan yi shiga irin ta mata a addinance. Sannan kuma bata fitar da tsaraicin ta a waje. Wajen tafiyar ta al’amura kuwa na rayuwa, Hadiza Gabon ba’a bar ta a baya ba, inda shima ta kasance daya tilo.

Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo masu yawa a masana’antar Kannywood. Sannan ta kasance Jakadiya ta kamfanin MTN a Najeriya. Bugu da kari ta kasance mace ta farko da ke tafiyar da gidauniya mai zaman kanta a masana’antar Kannywood mai suna Gidauniyar HAG (HAG Foundation) wanda kan bayar da tallafi ga yara kanana da mata marasa galihu a fannin ilimi, ciyarwa, lafiya da dai sauran su.

Kuruciya, Rayuwar Gida da ta ‘Yan Uwa

Hadiza Aliyu Gabon

Jaruma Gabon haifaffiyar garin Libreville ce na kasar Jamhuriyar Gabon. Mahaifinta Malam Aliyu ya kasance dattijo dan asalin Gabon. Ta bangaren mahaifiyar ta kuwa ta kasance Bafulatana daga jihar Adamawa a kasar Najeriya. Tayi karatun piramare gami da sakandare a kasar Gabon inda tayi jarrabawar gaba da sakandare da sha’awar zama lawya inda ta fara karatun digirin ta na farko a kan fannin lauyanci. Hadiza ta fice daga neman ilimin lawyanci a shekarar farko saboda wadansu dalilai da suka hana ta cigaba. Amma daga bisani ta samu kammala karatun difloma a harshen Faransanci wanda kuma hakan ya bata damar koyarwa a wata makaranta cikin harshen na Faransanci.

Hadiza Gabon na da ‘yan uwa wadan da suka hada da Malam Aliyu (mahaifi), Hajiya Halima (mahaifiya), Muhammad Umar (dan uwa), Aisha Umar (dan uwa), Zakari Ali (dan uwa), Issa Ali (dan uwa), Hamidou Ali (dan uwa), Hachimu Ali (dan uwa), Muhammad Ali (dan uwa), Dahirou Ali (dan uwa) da kuma Adam Ali (dan uwa).

Kasancewa Jaruma
Hadiza Gabon ta tsinci kanta a cikin masana’antar Kannywood a yayin da ta shiga garin Kaduna daga jihar Adamawa bayan samun sha’awa da tayi a citin masana’antar ta Kannywood tare da wata ‘yar uwarta. A wannan lokaci ne ta samu haduwa da Jarumi Ali Nuhu inda ta nemi taimakon sa gami da hadin kai domin zama Jaruma. Hadiza ta samu fita a shirin fim ta farko a rayuwar ta a cikin fim din Artabu a shekara ta 2009.

Lambar Yabo da ta Girma

Hadiza Gabon a Lokacin Kannywood MTN Award Kashi na Biyu a Abuja Najeriya.

Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo dana girma kala kala a masana’antar Kannywood. Ciki harda Fitacciyar Jaruma a masana’antar Nollywood a shekara ta 2013 a fim din ‘Babban Zaure’ da kuma Jaruma a taron ban girma na biyu a masana’antar Kannywood wanda akayi a shekarar 2014 a fim din ‘Daga Ni Sai Ke’. Mai Girma Gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso shima ya samu baiwa Jaruma Hadiza Gabon lambar yabo a shekara ta 2013.

Jaruma Hadiza Gabon ta dauki lambar girmamawa daga Kannywood AWA 24 Film & Merit Award a shekarar 2015 a fim din ta na ‘Ali Yaga Ali’. Sai kuma taron African Hollywood Awards shima data samu na fitacciyar Jaruma a shekara ta 2016 a fina finan Hausa na nahiyar Africa a cikin yaren Hausa.

Hukumar Gidan Malamai da aka fi sani da Kano State Senior Secondary Schools Management Board ita ma ta samu karrama Hadiza Aliyu Gabon a shekara ta 2016 a bisa gudummawar da ta kam bawa ilimi a Jihar Kano karkashin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Sai kungiyar Start Up Kano ina ta karrama Hadiza a shekara ta 2016 a bisa babbar gudummawa akan bayar da jari ga marasa aikin yi.

Aikin Gidauniyya
Hadiza Gabon ta fara aikin kafa gidauniya a shekara ta 2015 wanda kuma a cikin shekara ta 2016 tayi mata ragista. Gidauniya mai suna HAG Foundation anyi ta ne domin tallafawa mata da kananan yara marasa galihu a fannin ilimi, lafiya da abinci. Hadiza Gabon ta kasance mace ta farko a masana’antar Kannywood da ta fara bayar da irin wannan gudunmawa.

A watan Maris na 2016, Hadiza Gabon ta ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira a Jihar Kano wadanda rikicin Boko Haram ya ritsa dasu inda ta raba kayayyaki da suka hada da kayan abinci da sutura dama sauran ababan more rayuwa.

Shafukan Sada Zumunta
Website: http://www.hadizaaliyu.com/
Twitter: AdizatouGabon
Facebook: AdizatouGabon
Instagram: Adizatou
Wikipedia: Hadiza Aliyu

Shafuka masu alaka: Tarihin Rahama Sadau

7199total visits,1visits today


47 Responses to "Tarihin Hadiza Aliyu Gabon"

 1. Halima.   July 8, 2017 at 1:56 pm

  Hakkun nina shaida tanada girmama mutane don mun hadu umra da ita mungaisa sosai daita ba girman kai munyi hira da ita.Allah ya albarkace ta da baiwar da Allah ya bata tayi fice ya bata rayuwa ta addini ya bata miji na kwarai.

  Reply
 2. Hafsat Ermum   July 8, 2017 at 11:12 pm

  Tabbas daban take a masana’antar kannywood.Fatan mu Allah ya saka mata da alkhairi

  Reply
 3. shurala belayneh   July 8, 2017 at 11:13 pm

  wow yamral

  Reply
 4. Aboubakar Sourayath   July 9, 2017 at 1:55 am

  Moi je t’apprécie beaucoup et j’aimerai avoir ton numéro si ça te gêne pas car mon rêve sais d’être comme toi.

  Reply
 5. Dikko   July 9, 2017 at 6:50 am

  Allah ya baki miji na gari kiyi Aure

  Reply
  • haruna usman   September 27, 2017 at 10:48 am

   idan tanasona tasamu dama inason Indon Kauye

   Reply
 6. Haruna Zakariya   July 9, 2017 at 7:55 am

  Real and natural in her acting. Not fake.Myfavourite actress

  Reply
 7. Shehu Adamu   July 9, 2017 at 8:11 am

  Gaskia Ne Batada Matsala, Allah Ya Taimake Ta, Ya Karemata Martaban Ta

  Reply
 8. Rasheeda   July 9, 2017 at 8:34 am

  Ina mata fatan Alheri,kuma muma Allah bamu ikon taimaka wa wasu,Allah baki miji nagari

  Reply
 9. Abdullahi Abubakar zaki   July 9, 2017 at 9:45 am

  Agaskiya hadiza Gabon ta samu shaidu da dama agun al uma nima tazo garinmu kuma tayiwa mutane fara,a dasakin fuska Allah yataimaketa kuma yabata miji nagari

  Reply
 10. Akar Kolo   July 9, 2017 at 10:41 am

  Wallahi yanda kowa yana yaba ta nima ina yaba ta sosai.Fatana Allah ya bata sa’a kullum acikin abubuwan da take yi.

  Reply
 11. abubakar   July 9, 2017 at 12:04 pm

  Kwarai kuwa nima jarumatane INA yinta sosai kuma India nima zan samu Shiva kanywood movie da naji dadi

  Reply
 12. Idrissa sounna   July 9, 2017 at 12:13 pm

  Bon courage a toi salut

  Reply
 13. Auwal Haruna Bello   July 9, 2017 at 12:47 pm

  Allah yaqara taimakon Duk maitaimakawa al’umma__ameen summa ameen

  Reply
 14. Umar muhammad dabo   July 9, 2017 at 12:50 pm

  ttabbas jarumace wadda tae fice, ina mata fatan alkhairi da addu ar samun miji nagari, HAG FONDATION babban abin alfahari agaremu allah yasaqa mata da alkhairi

  Reply
 15. Mariam   July 9, 2017 at 10:08 pm

  Je t’apprecie enormement je prie Allah azzawadjel qu’il t donne un mari pieux

  Reply
 16. Ahmad Adamu Modibbo   July 9, 2017 at 10:25 pm

  Ina mata fatan alheri Allah ubangiji yakareta daga dukkannin sharrin abunda zai cuceta duniya da lahira

  Reply
 17. Shuaib   July 9, 2017 at 10:57 pm

  Nice, Hadiza. Keep it up.

  Reply
 18. jabeer Ahermad   July 10, 2017 at 1:24 am

  Allah sarki baiwar Allah hadiza gabon kici gaba da taimakama musulmai kema insha Allahu Allah zai taimakeki a dukkan lammuranki na yau da kullun kuma nima ina yimaki fatan Allah ya Albarkaci rayuwarki

  Reply
 19. Nasiru Adamu Kachallah   July 10, 2017 at 7:17 am

  Ina Miki Addu’a Allah Yataimakeki Kamar Yadda Kike Taimakawa Wasu,yasakamiki Da Aljannah,akarshe Shawarana Gareki Shine Idan Allah Yabaki Miji To Kiyi Aure Saboda Ba Abinda Ke Karemutuncin Mace Musulma Kamar Aure.

  Reply
 20. yunusa a hudu   July 10, 2017 at 9:55 am

  hadiza ALIYU Gabon Allah yabaki nasara

  Reply
 21. Gaddafi umar   July 10, 2017 at 5:03 pm

  Allah ya kara daukaka hajiya hadiza; Gaddafi muhd saraki

  Reply
 22. sa'adiya shehu   July 11, 2017 at 11:48 am

  Wow I lyk it

  Reply
 23. Zakariyya   July 11, 2017 at 3:11 pm

  Masha Allah Allah yakarba mata aiyukanta na alkhairi yakuma bata miji nagari

  Reply
 24. vkarami   July 11, 2017 at 8:22 pm

  Allah ubangiji yabiya da mafificiyar sakamakonsa Na Alkhairi, domin duk Wanda yataimaki mutane kuma y karrAmasu to shima Allah za karramashi, nice HAG. Allah yabaki mini nagari

  Reply
 25. Laouali danilla   July 12, 2017 at 3:12 pm

  Add your commentTu es pour moi une beaute dont je reve je t’admir eternellement.

  Reply
 26. Izziddin Abdullahi   July 12, 2017 at 5:31 pm

  Allah ya kawo miki miji nagari kiyi aure.Allah ya taimake ki akan harkar gidauniyarki.

  Reply
 27. Fatsuma T. Pindar   July 13, 2017 at 7:20 pm

  Masha Allah Hadiza A Gabon. Allah ya Taya ki Riqo amen. Allah Kuma ya Kade hau. Amen

  Reply
 28. Manirou Tanimoune   July 17, 2017 at 3:18 pm

  Ma shallah Hadiza wanan hakane ki na d’à masoya d’à dama anma ni na masaman ne

  Reply
 29. YUSUF SULAIMAN GABARIN   July 19, 2017 at 7:55 am

  Fatan alheri Allah yataimaki riko Ameeen

  Reply
 30. IBRAHIM ABBAS GWARZO   July 27, 2017 at 4:41 pm

  A GASKIYA SAIDAI NACE ALLAH YASA KIYI AURE DOMIN SHINE ADON YA MACE IDAN KIKA MUTU KINA HARKAR FILM BAKI DA ABINDA ZAKI KARE KANKI GURIN UBANGIJI ALLAH YASA MUDACE AMEN

  Reply
 31. Hafiz Koza   July 30, 2017 at 2:07 pm

  Tana samun yabo ta kowane vangare ba kaxan ba. Allah riqa mata tare da yi mata kariya daga dukkan abun qi.
  .
  Sai kuma wani xan tambihi da zan yi game da wannan fassara na tarihi da aka yi. Yana da kyau a yayin fassara abu ya kasance wanda ke karantawa ya kasa gane cewa fassara aka yi. Misali a wajen da kuka ce, ta ziyarci ‘gidan’ ‘yan gudun hijira… Ai ‘Sansani’ ake cewa ba gida ba. Sannan kun ce ‘…ba ta nuna al’aurar ta a waje.’ To shi kuma wannan wane irin abu ne gatsal haka! Me zai hana ku ce, ‘…ba ta shiga mai nuna tsiraici.’ Idan ma dole sai kun bayyana hakan?
  .
  Na gode Muryar Arewa. Ina jinjina muku sosai!

  Reply
  • Muryar Arewa   July 30, 2017 at 3:30 pm

   Mallam Hafiz Koza mun gode da gudunmawar da ka bamu wajen gyaran kalmomi a shafin Jaruma Hadiza Gabon. Muna masu farin cikin sanar maka cewar mun gamsu da gyaran da ka bayar kuma mun aiwatar da shi nan take.

   Allah Ya kara budi da daukaka, amin. Mun gode sosai.

   Reply
 32. Saa'diyya Sami   August 11, 2017 at 4:53 pm

  Dije naji an miki wani kirari wai ta masu gari. Mai wannan yake nufi? Ko kema kina da jinin sarauta a jikin ki bamu sani ba.

  Reply
 33. maryam idris   August 13, 2017 at 3:06 pm

  Compliment of great goes to u my belove actress.wish I can see u……..

  Reply
 34. Abdulmalik Rufau Zango   September 5, 2017 at 9:20 am

  Nima nashaida hakan malam ginbiya sarauniya Hadiza Gabon

  Reply
 35. muaz yusuf sunusi   November 22, 2017 at 12:38 pm

  Alhamdulillh nima ina mai yiwa auntyna adizatou fatan alkairi da kuma fatan allah ya qara daukaka ameen.
  Sannan kuma dan allah ni qarin haske nakeso nayi kuma ya xama saqo a gareta ita bbar aunty na, ”saqon kuwa shine dan mu damuke gefe da inda take dan allah a dan mu ba tasamu lokaci ta kawo mana ziyara inda muke wallahi muna mutuqar santa a kanta anayi mana dariya dan allah inhar da lokaci ta taimaka ta kawo mana xiyara munsan tanayi allah y kara basira, daukaka, tare da rayuwa mai amfani amin.nagode
  MUAZ YUSUF SUNUSI
  DANBAHAUSHE
  DAWAKIN TOFA L.G.A
  08125323116,09027769334

  Reply
 36. muaz yusuf sunusi   November 22, 2017 at 10:36 pm

  tabbas wannan hka yke Allah h qara daukaka auntyna

  Reply
 37. Abubakar Tulmi   December 6, 2017 at 6:38 pm

  Hadiza ki godema da duniya ta baki kyakkyawar shaida Allah ya taimakeki yakuma albarkace ki da miji nagari

  Reply
 38. sani abdullahi   December 28, 2017 at 9:19 pm

  gaskiya yaren yan jarumace mai ta shei

  Reply
 39. SANI MUSA BOMBOY   March 1, 2018 at 7:45 am

  fatan alkhairi agareki

  Reply
 40. Dahiru Adamu Abubakar   June 4, 2018 at 8:30 pm

  Allah saka

  Reply
 41. Abubakar   July 18, 2018 at 7:09 pm

  Jam sago

  Reply
 42. Fatimah Shuaib Musa   July 22, 2018 at 1:38 am

  May Allah continue to guide and protect you . Continue with the good work, Allah is with you.

  Reply
 43. Ahmad m Bature   August 10, 2018 at 12:32 pm

  alh yakara taimaka mata akan aikin alkairin da takeyi

  Reply
 44. Farida Mafara   November 8, 2018 at 8:59 pm

  Jarumata tadabance kuma ta mussaman halinta na kirki Allah yasakamata da gidan aljanna miji nagari Aamiin Allah yakara miki daukaka da tsawon kwana

  Reply
 45. muttaqa yakubu Dass   November 12, 2018 at 12:41 pm

  aslm jarumata allah kara basira ameen summa ameen

  Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.