Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 20 a Nigeria

Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya na cewa akalla mutane 20 ne suka mutu sannan fiye da 30 suka samu munanan raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake a garin Konduga.

Wasu mata ne guda uku suka kai harin a wata kasuwar sayar da raguna da ke unguwar Mandirari da yammacin ranar Talata.

An ce guda biyu daga cikin matan sun kai ga tayar da bama-baman da ke jikinsu, a inda jami’an tsaro suka harbe ta ukun kafin ta tayar da nata.

Matan sun kasu gida uku ne a bangarorin kasuwar daban-daban.

Har yanzu babu wata kungiya ko mutum da ya dauki alhakin kai wannan hari.

Sai dai kungiyar Boko Haram ta tsaurara kai irin wadannan hare-hare a ‘yan kwanakin nan.

Kuma hare-haren na zuwa ne a dai-dai lokacin da sojojin kasar suka sha yin ikrarin ganin bayan kungiyar.

Kazalika a farkon wannan watan ne manyan hafsoshin sojin kasar suka koma birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin kasar domin tunkarar wani gagarumin shiri na yakar kungiyar Boko Haram.

Wasu majiyoyin sun tabbatar wa da BBC cewa da yammacin ranar Talata, wasu ‘yan kunar-bakin-waken sun tayar da bam a yankin Aridamari da ke cikin birnin Maiduguri, sai dai kuma harin bai shafi kowa ba, a inda ya tashi da su kuma suka mutu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

709total visits,3visits today


Karanta:  Wasu Mata Biyu ‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Rasa Ransu A Maiduguri

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.