Hukumar Kula da Lamuran Sufuri Zata Kawo Tsimin Kudi

Kudurin da yanzu yake gaban majalisar dattawa idan ya zama doka za'a sami tsari mai kyau da hukumar da zata kula da lamuran sufuri a Najeriya hakan kuma zai kawo tsimin kudi.

Dan kwamitin sufuri na majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume shi ya bayyana hakan yayinda yake magana a taron sauraren ra’ayin jama’a kan kudurin kafa hukumar kula da lamuran sufurin Najeriya.

Kudurin ya zo daidai da lokacin da gwamnatin tarayya ta hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasa daga farkon badi.

Don nasarar kafa wannan hukumar a ra’ayin ministan sufuri Rotimi Amechi shi ne a mika aikin ga hukumar sufurin jiragen ruwa ta juye zuwa Hukumar Sufurin Najeriya domin kula da abubuwan da ake shigowa ko fita dasu ta hanyar teku.

Rotimi Amechi yace sun yi magana da majalisar wakilai wadda ta mikasu hannu kwararru domin sake duba kudurin wanda zai canza hukumar jiragen ruwa ta zama ita ce hukumar sufurin Najeriya.

Yayinda yake magana bayan taron, tsohon daraktan sayar da hannun jarin kamfunan gwamnatin Najeriya Ibrahim Muhammad Kashim yayi sharhi akan muradun gwamnatin Najeriya na son rage kashe kudi ta hanyar karawa hukumar hada hadar jiragen ruwa karfi ta zama mai kula da sufurin Najeriya maimakon kafa wata sabuwa. Yin hakan zai kara arzikin kasar fiye da abun da ake samu daga man fetur.

Ita hukumar hada hadar jiragen ruwa ta fadada ayyukanta da kafa tasoshin kan tudu don tallafawa wadanda ba sa gefen teku.

360total visits,1visits today


Karanta:  Babu Fasfo ga wanda bashi da katin dan kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.