Hukumar Kwastam Ta Yi Babban Kamu a Najeriya

Hukumar kwastam din Najeriya na ci gaba da samun nasara akan masu fasakori, na baya bayan nan shine motoci goma sha biyar da hukumar ta kama a yankin jihohin Oyo da Osun shake da kaya iri iri da kudinsu ya haura Naira miliyan 28.

Shugaban kwastan mai kula da jihohin biyu Udu Aka shi ya gabatarwa taron ‘yan jarida ababen da suka kama wadanda inda ya ba da kiyasin kayan.

Aka ya kara da cewa abun damuwa ne wasu ‘yan Najeriya marasa kishin kasa sun ki tuba da yin fasakorin kayayyaki duk da gargadin da ake yi masu da asarar da suke tafkawa.

Har ila yau ya kuma ce abun takaici ne wasu mutane musamman dattawa suna zuwa su yi kamun kafa domin a saki haramtattun kayayyakin da aka kama.

Aka ya ci gaba da cewa a tsarin gwamnatin tarayya an hana shigowa da shinkafa ta iyakokin kasa saboda inganta tattalin arzikin kasa.

Haka ma an hana shigowa da tsoffin tayoyi saboda kare lafiyar jama’a tare da inganta ma’aikatun dake sarrafa tayoyi a cikin gida.

Asalin Labari:

VOA Hausa

599total visits,2visits today


Karanta:  An kama bindigogi sama da dubu daya a Lagos

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.