Hukumar zaben Nigeria ta fara shirin kiranyen Melaye

A Najeriya hukumar zaben kasar ta fitar da jadawalin farko mai matakai shida da za ta bi domin yi wa sanata Dino Melaye kiranye.

A cewar jadawalin wanda hukumar ta wallafa a shafinta na twitter, a ranar Litinin mai zuwa ne za ta kafe takardar sanarwa kan tantante masu bukatar a yi wa sanatan kiranye a ofishinta da ke mazabarsa a birnin Lokoja a jihar Kogi.

Haka kuma ta sanya ranar 31 ga watan Yulin da muke ciki ta zamo ranar karshe da masu sa ido za su mika bukatar yin haka ga hukumar.

Jadawalin ya kuma bayyana cewa a ranar 10 ga watan Agusta ne kuma rana ta karshe ta karbar sunayen wakilan da za su sa ido a tantancewar daga bangaren sanata Melaye da kuma masu bukatar a yi masa kiranye.

Taron masu ruwa da tsaki zai biyo baya a ofishin hukumar na jiha a ranar 15 ga watan na Agusta, sai ranar 19 Agusta wadda za aiwatar da tantancewa a dukkanin runfunan zaben da ke mazabar sanatan.

Hukumar ta kuma ce za ta fitar da wani jadawali kan ranar da za a yi zaben rabagardamar, bayan ta fitar da sakamakon tantance masu kada kuri’ar a ranar ta 19 ga watan Agusta.

A ranar 22 ga watan Yunin da ya gabata ne dai hukumar ta karbi takardar sa hannun mutum kusan 200,000 daga mazabar Kogi ta yamma, wadanda suka bukaci a yiwa sanata Dino Melaye kiranye.

Lamarin da ya yi watsi da shi da cewa wani ‘wasan kwaikwayo ne’.

Inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ce ke ingiza masu bukatar kiranye, saboda ba ta son sukar da sanatan ke yi mata kan maganar rashin biyan albashin ma’aikata.

Karanta:  Nigeria ta daukaka kara kan wanke Bukola Saraki
Asalin Labari:

BBC Hausa

557total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.