Hukumar zaben Nigeria za ta duba batun yi wa Melaye kiranye

Hukumar zaben Najeriya ta tabbatar da karbar takardar sa hannun kusan mutum 200,000 daga mazabar Kogi ta yamma, domin yi wa sanata Dino Melaye kiranye .

Sakataren yada labarai na shugaban hukumar, Rotimi Oyekanmi ya shaida wa BBC cewa abu na gaba da hukumar za ta yi shi ne sanya rana domin tantance sa hannun mutanen da suka fito daga mazabar sanatan.

A ranar Alhamis ne hukumar ke yin wani taro wanda kuma a yayin taron ne za ta sanya ranar tantance sa hannun.

Mutanen mazabar dai na neman kiranyen sanata Melaye ne bisa zarginsa da rashin yi musu wakilci mai inganci a majalisar dattawa.

Suna kuma yi masa zargin cewa, baya zuwa mazabarsa domin ganawa da mutane, don sanin halin da suke ciki.

Sai dai a nasa martanin Dino ya ce batun kiranyen nasa “wasan kwaikwayo ne”, in da ya zargi gwamnan jiharsa ta Kogi, Yahaya Bello da kitsa kiranyen.

Dino ya shedawa BBC cewa, gwamnan baya farin ciki da sukar da ya ke yi masa a kan rashin biyan albashin ma’aikata, da rashin biyan fansho da kuma rufe makarantu na tsawon watanni a jihar.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin bangaren gwamnan, amma kawo yanzu ba ta yi nasara ba.

An dade ana zaman doya da manja tsakanin sanatan mai janyo kace-nace da kuma gwamnan jiharsa Kogi.

Ko a baya-baya nan magoya bayan bangarorin biyu sun yi zanga-zangar goyon bayan gwanayen na su a Lokoja, babban birnin jihar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

384total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.