Ina nan da ƙafafuwa na — Zainab Indomie

Fitacciyar mai fitowa a fina-finan Hausa Zainab Indomie, ta ƙaryarta labarin da ake yaɗa wa cewa an yanke mata ƙafa.

A sanarwar da ta wallafa a shafinta na sada zumunta na Instangram ta ce, hoton da ake yaɗawa da ƙafa ɗaya, na wani fim ne da ta yi mai suna Ɗinyar Makaho.

Jarumar ta yi roƙo da masu yi mata mummunan fata a rayuwa su daina, sannan ta ƙara da cewa iftila’in rayuwa na iya faɗuwa kan kowa, amma ba a riƙa yi mata ƙage ba.

A baya-bayan nan dai ana ta yaɗa hotunan jarumar da ƙafa ɗaya a yanke, a kuma zaune a gadon asibiti, a dandalin sada zumunta da muhawara na intanet da kuma Whats app, a inda ake danganta abin da ya same ta ga sakamakon ubangiji na abubuwan da ta ke yi a rayuwa.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1421total visits,1visits today


Karanta:  Beyonce: Hoton Sir Carter da Rumi Ya Bayyana

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.