Ina samun sauki sosai — Shugaba Muhammadu Buhari

Shuagban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana samun sauki sosai, kuma da zarar likitoci sun ba shi dama zai koma gida domin ci gaba da ayyukansa.

A wata hira ta wayar tarho da Shugaban kasar Guinea Alpha Conde, Shugaba Buhari ya yabawa al’ummar kasar bisa addu’ar da yan kasar suka yi masa ta samun lafiya a cikin makon jiya.

Wannan na zuwa kwana guda bayan da gwamnan jihar Imo ya shaida wa BBC cewa shugaban zai koma gida nan da mako biyu.

Kusan kwana 80 kenan da Shugaba Buhari ke jinya a birnin Landan kan cutar da ba a bayyana ba kawo yanzu.

Me wasikar ta kunsa?

A cikin wasikar mai kwanan watan 24 ga watan Yulin 2017, Shugaba Buhari wanda tun farko ya yi magana da Alpha Conde ta wayar tarho a matsayinsa na shugaban Tarayyar Afirka ya ce, “Na gode bisa kirki da hangen nesanka wajen shirya addu’o’in kasa gaba daya don neman Allah ya ba ni lafiya.”

“Karimci ne da har abada zan rika tunawa da kuma yin alfahari da shi.”

“Ranka ya dade, za ka yi farin ciki da jin cewa ina kara samun lafiya, kuma da zarar likitoci sun ba ni shawara, zan koma kan ayyukana, na ci gaba da hidimtawa al’ummar Najeriya da suka zabe ni, kuma a kullum suke mini addu’o’in samun sauki.”

Wasikar ta ci gaba da cewa tun da farko, Shugaba Buhari ya kuma amince da zabarsa a matsayin jagoran “yaki da cin hanci da rashawa a taon Tarayyar Afirka na shekarar 2018”, wanda shugabannin kasashen kungiyar suka yi a wani taronsu karo na 29 ranar 4 ga watan Yuli a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Asalin Labari:

BBC Hausa

410total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.