Buratai Na Son Shekau A Mace Ko A Raye

Shugaban Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya bawa Operation Lafiya Dole wa'adin kwanaki 40 ta kawo masa Shekau a mace ko a raye.

A ranar juma’a 21, ga watan yuli, shugaban rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya umurci shugaban rundunar dake yaki da boko haram ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Ibrahim Attahiru wa’adin kwanaki arba’in ya kawo masa shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar shekau a mace ko a raye.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Burgediya Janar Sani Kukasheka Usman, ya bayyana cewa babban hafsan sojojin ya umurci rundunar da ta tabbatar ta zakulo Abubakar Shekau a duk inda yake cikin wadannan kwanaki 40 ko da rai ko ba rai.

Ya kuma bukaci al’umma da ta taimaka da duk wasu bayanai da zasu taimaka wajan gudanar da wannan aiki.

Kungiyar ta Boko Haram dai ta samu rauni ne a baya bayan nan sanadin kai hare hare da sojojin Najeriya suke kaiwa cikin dagin Sambisa inda kuma suka sami nasarar kwace kuraren da ‘yan kungiyar ke rike dasu a baya.

Asalin Labari:

Muryar Arewa da VOA Hausa

1593total visits,1visits today


Karanta:  An sake kaddamar da kamfanin jirgin saman Najeriya a Birtaniya

One Response to "Buratai Na Son Shekau A Mace Ko A Raye"

  1. Abdulkadir nafi u   July 22, 2017 at 2:41 pm

    Maza maganin maza

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.