India: Ya kashe matarsa saboda lattin kin dafa abincin dare

‘Yan sanda a kasar India sun ce sun cafke wani dattijo mai shekara 60 da ya hallaka matarsa ta hanyar bindigewa saboda bata gama abincin dare da wuri ba.

A daren Asabar ne Ashok Kumar ya dawo gida cikin maye, inda gardama ta kaure tsakaninsa da matarsa , kamar yadda wani babban jami’in ‘yan sanda Rupesh Singh ya shaida wa BBC a birnin Ghaziabad da ke kusa da Delhi babban birnin kasar.

An garzaya da Sunaina, mai shekara 55 zuwa asibiti bayan da ta samu rauni daga harbin bindigar da ta samu a ka, amma kafin a isa asibiti rai ya yi halinsa.

Mr Kumar ya amsa laifin da ya aikata, kuma yanzu haka yana cikin nadama, in ji Mr Singh.

” Mutumin ( Mr Kumar) ya saba shaye-shaye a kullum. A ranar Asabar ya dawo gida a buge, inda ya fara sa-in-sa da matarsa. Ta cika da bacin rai game da dabi’arsa, tana so ta yi masa magana a kai, amma ya bukaci ta kawo masa abinci da wurwuri,” in ji Mr Singh.

Ya kara da cewa ” Ya fusata da bata lokacin da ta yi kawai sai ya harbe ta”.

Wakiliyar BBC a birnin Delhi ta ce irin wannan cin zarafi da mata ke fuskanta a gidajen aurensu ba sabon abu bane a kasar ta India- yana faruwa a ko ina a fadin duniya- amma abinda ya banbanta India da sauran kasashe shine dabi’ar rashin fitowa fili a bayyana.

Asalin Labari:

BBC Hausa

837total visits,1visits today


One Response to "India: Ya kashe matarsa saboda lattin kin dafa abincin dare"

  1. Abubakar sanni   July 11, 2017 at 1:48 pm

    Allah yakyauta kalubale ga iyaye masu ya’ya mata in zaku aurar da ya’yanku kubincika kutabbatar mijin baya shaye shayen giya da dai sauransu

    gani gawane ance ya ishiwane tsoron Allah

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.