INEC ta dage kiranyen Melaye

Hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta dage shirin da take yi na tantance takardun neman kiranye da ta shirya za ta yi a kan dan majalisar dattawa Dino Melaye.

Hukumar ta fitar da wannan bayanin ne bayan da ta sami umarni daga wata kotu na ta dakatar da shirin nata.

Hukumar ta INEC ta ce, “A matsayinmu na hukuma mai mutunta bangaren shari’a, mun yanke shawarar bin umarnin kotu”.

Amma hukumar ta ce za ta ci gaba da neman kotun ta janye umarnin, kuma ta saurari karar cikin kankanin lokaci.

Sanata Dino Melaye na wakiltar mazabar Kogi ta Yamma ce a majalisar dattawan Najeriya tun watan Mayun shekarar 2015.

Wata babbar kotu a birnin Abuja ta bayar da umarnin dakatar da shirin yin zaben kiranyen ne bayan da mutumin da lamarin ya shafa, Dino Melaye ya shigar da kara inda yake neman kotun ta hana hukumar gudanar da zaben.

Mutanen da sanatan yake wakilta sun tuhume shi da rashin cika alkawurran da yayi musu, da kuma bacewar da ya yi daga mazabar tun bayan zaben da suka yi masa a shekarar 2015.

A cikin watan Yuni masu kada kuri’a daga mazabar sanatan daga jihar Kogi suka mika kudurinsu na yi wa dan majalisar kiranye ga hukumar ta INEC.

A ranar 3 ga watan Yuli kuma hukumar INEC ta tantance bayanan wadanda suka sanya hannunsu a takardun kudurin da ke neman yi wa sanatan kiranye.

Daga baya kuma a ranar 10 ga watan Yuli, hukumar INEC ta fitar da shirinta na tantance takardun neman kiranyen duk da cewa sanatan ya garzaya kotu domin dakatar da shi.

Amma akwai wani hanzari ba gudu ba, domin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa hukumar INEC damar kammala zaben kiranye a cikin kwana 90 daga ranar da a ka gabatar da takardu koke daga mazabar dan majalisar da abin ya shafa.

Karanta:  Majalisar Dattawan Najeriya Ta Gamsu da Yadda Hukumar EFCC Ke Yin Aikinta

Da alama hukumar ta INEC za ta daukaka kara domin ta ce za ta, “Ci gaba da aikin da tsarin mulkin Najeriya ya dora mana”.

Dino Melaye ya dade yana cewa ana shirin yi masa kiranye ne domin cimma wata bukata ta siyasa.

Ya zargi gwamnan Kogi Yahaya Bello da kitsa yunkurin yi masa kiranyen.

Gwamnan da Sanata Dino Melaye ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin kasar ce, amma sun dade suna kai ruwa rana.

Dokar zaben kasar ta ce ana bukatar sa hannun a kalla rabin masu rajistar yin zabe daga mazabar da ke neman yi wa dan majalisa kiranye kafin batun ya sami karbuwa.

Akalla masu kada kuri’a 188,588 suka sanya hannu a kan takardun neman yi wa sanatan kiranye.

Wannan na nufin cewa an sami fiye da rabin masu kada kuri’ar mazabar wadanda yawansu ya kai 360,098.

Asalin Labari:

BBC Hausa

5227total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.