IPOB: Sanatoci Zasu Gana Da Shugabannin Tsaron Kasa

Daga Abuja – Shugaban Majalisar Dattijai ta Kasa, Dr Bukola Saraki yace majalisar zata gana da Shugabannin Tsaron Kasar nan don tsara hanyar magance rikice-rikicen da suka haifar da tashin hankali a Kudu Masu Gabashin Kasar.

Yace ana tsammanin ganawar nan bada dadewa ba, haka kuma ganawar zata maida hankali kan tashin hankalin da ke akwai a Kudu Masu Gabashin Kasar harma da abin da yabiyo baya na fada a Filato.

Saraki a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahdi a Abuja yace, jami’an tsaro, shugabanin siyasa dana addini dole ne suyi aikin samar da kafar tattaunawa wadda zata magance kalubalantar juna don samar da zaman lafiya a kasa bakidaya.

Sanarwar da Babban Mai taimaka masa ta harkokin yada labarai, Yusuph Olaniyonu ya fitar ta bukaci duk ‘yan Nijeriya dasu zauna lafiya su kuma bar duk wasu maganganu ko ayyukan da zasu iya tayar da hankali a sassan kasar.

Shugaban Majalisar Dattijan yace tashin hankulan dake faruwa a kasar baya rasa nasaba da kalubalan tattalin arzikin da ‘yan kasar nan ke fuskanta.

“Tashin hankalin dake faruwa a wasu sassan kasar nada asali da yanayin da tattalin arziki ke ciki.

“Al’ummar kasar nan su tabbatar cewa wasu daga cikin ayyukan da majalisar dokoki da majalisar zartarwa keyi don warware matsalolin tattalin arziki sun fara haifar da sakamako mai kyau.

“Wannan shi yasa kwanannan muka shaida dawowar tattalin arziki dama fitar kasar nan daga cikin kamfar tattalin arziki,” a cewarsa.

Yayi kira da jama’a dasu kwantar da hankalinsu, musamman ma a kudu masu gabashin kasar da jihar Filato inda yake cewa gwamnati na bukatar hadin kan kowa wajen magance dukkanin matsaloli.
“Ina rokon mutanenmu dasu kauracewa rura wutar rikicin kabilanci da addini. Bai dace mu kara fadada matsalolin da kasarnan  ke ciki ba mu sanya al’umma cikin hatsari da tashin hankali da dorar da rikici a kasa

Karanta:  Ana daf da wancakali da Kuraye da Diloli daga Gwamnati - Aisha Buhari

“Gwamnati na bukatar gudunmowar duk ‘yan Nijeriya don haka mu taimaka wajen samar da zaman lafiya. Babu wani cigaba ko wani tattalin arzikin da zai samu a karkashin rikici ko rashin zaman lafiya.

“Zuba Jari da cigaba na samuwa ne kawai idan akwai zaman lafiya,” a cewar Sarakin.

Ya shawarci shugabanin siyasa, shugabanin addinai da shugabannin al’umma dasu dauki matakan da suka dace wajen kawo karshen rikicin da kuma tabbatarwa mutane cewa hanyar da tafi ita ce mu zauna lafiya da jituwa da juna.

“Dole ne dukkan shugabanni su goyawa gwamnati baya su kuma yi kiran azauna lafiya, da son juna dama jituwa da juna.

Ya kara da cewa, “Ina kara kira ga mutanenmu dasu bar daukan doka a hannunsu dama tsokanar abokan zama.”

NAN

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

6668total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.