Iran ta bi sawun North Korea, inda tayi gwajin sabon makami mai linzami

Kamar kasar North Korea, Iran itama tayi gwajin wani sabon makami mai linzami wanda aka rawaito cewa ka iya daukan kawuna yaki da dama, inda aka bayyana nasarar gwajin ranar Jumma’a a gurin faretin soji a Tehran.

Makamin wanda aka fi sani da suna “Khorramshahr” na cin tsahon zangon mil 1,250 (kilomita 2000) zai kuma iya daukan kawuna yaki da dama kamar yadda majiyar press TV ta bayyana.

“An harba makamin Khorramshahr daga wani gurin da ba a bayyana ko ina ne ba, kuma a kirance karami ne sai dai ya keru sosai wanda za a iya sarrafa shi a dan karamin lokaci,” kamar yadda majiyar yada labaran ta bayyana.

Da wannan tsahon zangon ne, makamin zai iya kaiwa ga kasar Israel da Saudi Arabiyya a saukake.

Yayin da yake magana ranar Jumma’a a gurin faretin sojoji, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani yace Tehran zata cigaba da inganta makamin nukiliyarta dama inganta tsaron sojinta

“Zamu habaka tsaron kasarmu da karfin sojinmu duk lokacin da muka ga hakan ya zama dole,” a cewar Rouhani. “Bama bukatar iznin kowa wajen kare kasarmu.”

Ya kara da cewa, “Ko ana so ko ba a so zamu taimakawa Siriya, Yemen da Palasdin, haka kuma zamu habaka makamin kare dangin mu.”

Rahouni yace kasar Amurka da Israel sun kebance kansu wajen adawa da yarjejeniyar nukilayar da aka kulla ta shekarar 2015 tsakanin kasar Iran da wasu kasashe. Ya kara da cewa Iran ta cigaba da cika alkawarinta, a cewar kafa yada labarai ta Press TV

Kasar Amurka dai ta tsawaita saukin takunkumin da ta sakawa kasar Iran satin da ya wuce wanda wani bangare ne na cikin yarjejeniyar, wadda shugaba Donald Trump  ya bayyana da “mafi mauni wanda ba a taba gani ba”

Karanta:  Al-Shabaab ta kama wani yanki mai arzikin uranium a Somalia

Hanya ce mai sarkakiya, amma tayi ma’ana tunda sake sakawa Iran tukunkumi zai kai ga kasar ta kawo karshen yin biyayya ga yarjejeniyar ta kuma sake komawa kan matsayinta na sarrafa makamashin yuraniyon, barazanar da Iran ka iya dauka in dai Amurkan tayi waiwaye kan matsayinta na baya.

NAN

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

807total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.