Iran ta yi gwajin sabon makami mai linzami

Iran ta ce ta yi nasarar gwada sabon makaminta mai linzami kirar Khorram Shahr.

An bayyana makamin a wani faretin soja da aka gudanar jiya Juma’a a birnin Teheran kuma an ce yana iya cin nisan kilomita dubu biyu, idan an harba shi.

Tashar talbijin din kasar ta nuna hotunan gwajin da aka yi.

Wani makamin Khorramshahr da Iran ta gwada a watan Janairu ya yi bindiga yana cikin tafiya a sama.

Gwaji na baya-bayan nan ya zo ‘yan kwanaki bayan Shugaban Amurka Trump ya soki lamirin shirin Iran na kera makamai masu linzami a jawabin da ya gabatar cikin Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

6325total visits,3visits today


Karanta:  Mutane Milliyan 9 a Afrika Na Iya Mutuwa Saboda Katse Tallafin HIV

Leave a Reply

Your email address will not be published.