Isra’ila Ta Kori Wasu Falasdinawa Daga Gabashin Birnin Qudus

'Yan sandan Israila sun kori wasu iyalai Falasdinawa daga gidansu da ke Gabashin birnin Qudus, wanda aka kwashe shekaru ana takaddama a kansa.

Iyalan Shamasneh sun fice daga gidan, wanda suka kwashe shekara 53 a cikinsa, bayan wasu kotunan Isra’ila sun yanke hukuncin cewa gidan mallakin Yahudawa ne.

Dokokin Isra’ila sun amincewa dan kasar ya sake mallakar fili ko gidan da ya rasa bayan Jordan ta mamaye Gabashin Qudus a yakin da aka yi a 1948-9.

Isra’ila ta mamaye yankin tun lokacin da ta fatattaki Jordan a 1967.

Ranar Talata da safe, an tura ‘yan sanda gundumar Sheikh Jarrah d a lokacin da jami’ai ke korar iyalin Shamasneh daga gidan.

Kafofin watsa labarai sun ce iyalin su shida, cikinsu har da mai shekara sama da tamanin, sun fice daga gidan suka tsaya a waje tare da masu fafautika.

“Wannan ba karamin cinzali ba ne,” in ji Fahamiya Shamasneh, mai shekara 75, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP. “Watakila za mu rika yin bacci a kan titi.”

Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito cewa daya daga cikin mutanen da aka kora ya yi yunkurin fasa saman gidan ya koma ciki amma jami’an tsaro sun hana shi, inda suka yi barazanar kama shi.

Yahudawan da aka bai wa gidan sun koma cikinsa bayan an kori Falasdinawan.

Asalin Labari:

BBC Hausa

524total visits,1visits today


Karanta:  An lakadawa 'yan majalisar Venezuela duka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.