Isra’ila zata rufe tashar Aljazeera a fadin kasar

Benyamin Netanyahu

Isra’ila ta bayyana shirin ta na rufe tashar Aljazeera a fadin kasar saboda abinda ta kira yadda kafar yada labaran ke tinzira jama’a.

Ministan sadarwa Ayoob Kara daga Jam’iyyar Likud ta Benjamin Netanyahu ya ce tashar Al Jazeera ta zama wata kafar farfaganda ga kungiyar mayakan ISIS da kuma tinzira rikici tsakanin matasan kasar.

Ministan ya ce kusan daukacin kasashen da ke Yankin da suka hada da Saudi Arabia da Masar da Jordan sun bayyana tashar Aljazeera a matsayin mai tada hanakali.

A ranar 27 ga watan Yuli, Firaminista Benjamin Netanyahu, ya bayyana aniyar sa na rufe tashar lokacin da aka samu arangama tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Isra’ila dangane da tsauraran matakan tsaro a Masallacin Birnin Kudus.

Asalin Labari:

RFI Hausa

554total visits,1visits today


Karanta:  Amurka ta gargadi Syria kan hari da sinadari mai guba

Leave a Reply

Your email address will not be published.