Jacob Zuma ya Tsallake Rijiya da Baya

Pro-Zuma supporters celebrate after the vote of no confidence against the president was defeated.

Shugaba Jacob Zuma ya tsallake kuri’ar raba gardama da majalisar dokokin Afrika ta Kudu ta kada a yau Talata domin tsigeshi daga kan karagar mulki a bisa zargin cin hanci da rashawa da jam’iyyar adawa Democratic Alliance ta fitar.

‘Yan jam’iyyar ANC mai mulki a kasar sunyi ta wake wake da kade kade a yayin da aka sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a cikin sirri inda kuma magoya bayan jam’iyyar ANC suka fara shagalin murnar tsallakewa da Zuma yayi.

Kakakin majalisar, Baleka Mbete ta sanar da sakamakon inda ta bayyana cewar dokar bata samu rinjaye ba da akalla kuri’u 177 wadanda suke goyon bayan tsigeshi da kuma 198 na wadanda basu amince ba. Mutum tara daga cikin ‘yan majalisar babu samu kada kuri’ar ba. Duka kuri’un dai sun kama 384.

Kudin kasar dai wato Rand darajar sa ta dafi da kawo daya (1%) bayan an sanar da sakamakon kuri’ar.

Uwar jam’iyyar a nata jawabin bayan sanarwar ta jaddada cewar ba zata taba amince wa da duk wani kuduri da zai kawo nakasa a kasar ba.

Bayan ya tallake, shugaba Zuma ya shaidawa magoya bayan sa cewar jam’iyyar sa ta “ANC tana nan, kuma da karfin ta, sannan zaiyi wahala a karya ANC”.

1121total visits,6visits today


Karanta:  Wani mutum ya kashe matarsa saboda ta yi masa dariya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.