Jam’iyyar APC ta Lashe Zabukan Jihar Legas

Jam’iyyar mulki a Najeriya dama jihar Legas baki daya ta lashe ilahirin zabukan da aka gabatar na kananan hukumomi wanda akayi a ranar Asabar data gabata.

Jaridar Punch ta ruwaito cewar jam’iyyar All Progressives Congress a lashe zabukan a kananan hukumomi 20 dake jihar Legas da kuma gundumomi 37 duka dai a cikin jihar.

Sakamakon farko da gidan talabijin ta jihar ya fitar ya nuna cewa jam’iyyar ta All Progressives Congress  kusan ta dauke sakamakon zabukan wadanda suka hada da kananan hukumomin Ojokoro, Eti Osa, Lagos Island, Badagry Central, Onigbongbo, Odiolowo/Ojuwoye, Ikorodu West, Ejigbo, Ikeja, Ikorodu, Epe, Lagos Island East, Badagry West, Surulere, Ikorodu Central, Ikoyi/Obalende, Agboyi-Ketu, Eredo da dai sauransu.

Haka zalika jam’iyyar ta APC ta lashe zaben gundumar Papa Epe inda gwamnan na jihar ta Legas ya fito.

A cewar gwamnan na Legas wannan shine karo na farko da aka gudanar da zabe a cikin wannan jiha ta su. Ya kara da cewa akwai bukatar zage dantse wajen ganin cewar an tabbatar da demokaradiya a jihar Legas dama Najeriya baki daya.

1394total visits,1visits today


Karanta:  Dan Arewa Na Farko Ya Tsaya Takarar Shugabancin Karamar Hukuma A Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.