Jam’iyyar PDP na baikon Atiku Abubakar

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP reshen jihar Adamawa ta bayyana cewar zata tuntubi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar domin dawo dashi cikin jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar reshen na Adamawa Alhaji Abdulrahman Bobboi ya bayyana hakan a yayin da yake amsa tambayoyi ga ‘yan jarida a wajen wani taro a garin Yola dake jihar Adamawa.

Bobboiya kara da cewa baikon na Atiku zai taimakawa jam’iyyar PDP wajen gina Nijeriya. Ya ci gaba da cewa Atiku Abubakar bai amfana da zaman sa cikin jam’iyyar APC ba, don haka akwai bukatar dawowar sa cikin jam’iyyar PDP inda ake bukatar aikinsa.

“Atiku yana daya wadan da suka kafa jam’iyyar don haka muna son sa ya dawo, kuma ba zamu barshi ya numfasa ba har sai ya dawo. Zamu ci gaba da bibiyar sa tunda daga matakin mazaba har domin daowar sa.”

Shugaban ya yabawa hukuncin kotun koli kan tabbatar da Ahmed Makarfi a matsayin shugaban riko na jam’iyyar.

2064total visits,3visits today


Karanta:  Burin Kwankwaso Na Tsayawa Takarar Shugaban Kasa Na Daga Cikin Abin Da Ya Haifar Da Baraka A Kano - Sanata Barau

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.