Priyanka Chopra Da Rahama Sadau Zasu Gana

Fitacciyar Jarumar Masana’antar shirya Fina-finan Bollywood Priyanka Chopra na fatan haduwa da Jarumar Fina-finan Hausa ta Kannywood Rahma Sadau a dan wani lokaci kadan mai zuwa.

Tun farko Jaruma Rahama Sadau ce ta aika da sakon bankadar mafarkinta a fejin Priyanka na Twitter kan irin mafarkin da take da shi na kasancewa kamar Jaruma Chopra. Sakon wanda Jarumar ta rubuta kamar haka “Idan na duba nasarar da kika cimma, tana bani karin gwiwa na zama kamarki” – inji Sadau zuwa ga Chopra.

Sadau ta samu amsar kalmominta ‘yan dakikoki kadan daga Chopra wadda ta ba ta alwashin cewar “Ina godiya Rahama Sadau. Ina Fatan haduwa da ke nan gaba. Fatan alheri da kauna kan komai” – Inji Jaruma Priyanka Chopra.

Jaruma Sadau ta nuna murnarta matuka kan samun wannan amsa tare da ayyana cewar tana nan tana jiran lokaci. Sadau dai ta dade da kaunar wannan jaruma a ranta, wanda har ta kai ana mata lakabi da sunan Jarumar wato Priyanka Chopra ta Kannywood.

2127total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.