‘Jawabin Buhari Yayi Hannun Riga Da Halin Da Ake Ciki a Nigeria’

Jawabin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata, yana ci gaba da jan hankalin wasu 'yan kasar musamman a shafukan sada zumunta.

Yayin da wasu ke ganin cewa shugaban bai yi daidai ba, wasu gani suke ya yi abin da ya kamata.

Osasu Igbinedion gani take ya kamata Shugaba Buhari ya warkar da kansa kafin ya nemi bai wa makwabtansa magani.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, ‘yar Najeriyar ta ce: “Jawabin Buhari a zauren Majalisar Dinkin Duniya wani lamari ne na cire datti a idon makwabci, gabanin mutum ya cire daga nasa idon.”

Shima Onye Nkuzi ya ce jawabin shugaban Najeriyar ya yi hannun riga da abin da yake faruwa a kasarsa.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce jawabin shugaban bai zo da mamaki ba, yana mai karkare sakon da tambayan kan cewar “kwana nawa shugaban ya yi a Najeriya cikin wannan shekarar?”

Sai dai kuma, Ezeaka Chidozie ya mayar da hankali kan zargin adadin motocin da Shugaba Buhari ya tafi da su birnin New York, idan aka kwatana da na tsohon Shugaban Kasar Goodluck Jonathan a lokacinsa.

Ya ce yayin da Buhari ya je da motoci hudu, motocin da tsohon “Shugaba Jonathan ya isa wurin ne da motoci 30.”

Linus Hagher ya ce “duka nahiyar Afirka tana tare da Shugaba Buhari yayin da yake gabatar da jawabi a gaban zauren majalisar. Amma wadansu ‘yan Najeriya suna nuna rashin jin dadinsu game da jawabin.”

963total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.