Kaduna za ta Gurfanar da ‘Yan Sara Suka a Kotu

Gwamnatin Jihar Kaduna za ta gurfanar da wasu ‘yan kungiyar ta’addanci wadda aka fi sani da ‘Yan Sara Suka a kotu. Sanarwar ta biyo baya ne sakamakon zaman da Kwamitin Tsaro na Jihar ya gabatar a Jihar ta Kaduna a ranar ashirin ga watan Yuli (20 July 2017).

‘Yan ta’addar dai an samu kama yawa yawan su ne sakamakon wani samame da ma’aikata tsaro suka kai a shiyoyin Kaduna da Zariya.

A cewar Kwamitin Tsaro na Jihar ta Kaduna za’a tuhume su da laifin tayar da zaune tsaye da kuma asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Bugu da kari zasu gurfana a gaban Kuliya bisa laifuka da suka shafi rike makamai ba bisa ka’ida ba, damun al’umma tare da yin taro ba bisa ka’ida ba.

https://twitter.com/GovKaduna/status/888419480564641792

796total visits,1visits today


Karanta:  Hukumar SSS Ta Damke Wasu Kwamandojin Kungiyar Boko Haram

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.