Jihar Kano Na Zaman Makokin Rasuwar Dan Masani

Al’ummar Jihar Kano a arewacin Najeriya na zaman makokin rashin Dattijo Alhaji Dr. Maitama Sule Dan Masanin Kano wanda ya rasu a ranar 2 ga watan Juli na 2017 a birnin Alkahira na kasar Misra bayan wata ‘yar gajeriyar rashin lafiya.

Marigari Dr. Maitama Sule ya kasance a yayin rayuwar sa hazikin mutum kuma mai kishin al’ummar Najeriya baki daya ba tare da nuna banbancin siyasa ko jinsa ba.

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta samu bayar da hutun kwana daya a yau Talata 4 ga watan Juli na 2017.

Za’ayi jana’izar marigayin da misalin karfe biyu na rana a fadar Mai Martaba Sarkin Kano dake Kofar Kudu.

454total visits,3visits today


Karanta:  Igbo Mazauna Adamawa Na Goyon Bayan Najeriya a Matsayin Kasa Daya

Leave a Reply

Your email address will not be published.