Jirgi mai samar da intanet ya yi tashi na biyu

Facebook ya kammala gwada wani jirgin da ya ƙera maras matuƙi da ke amfani da hasken rana a karo na biyu, don samar da intanet ga yankuna masu rata na duniya.

Jirgin – wanda aka yi wa laƙabin Aquila – ya tashi tsawon sa’a ɗaya da minti 46 a cikin yankin Arizona na Amurka.

A gwajin da Aquila ya yi na farko cikin bazarar da ta gabata, iska mai ƙarfi ta jigata shi, inda ya faɗo a lokacin sauka.

Wannan karo, jirgin ya luluƙa sama tsawon ƙafa 3,000, ƙasa da burin kamfanin Facebook na ƙafa 60,000 a sararin samaniya.

Kamfanin sada zumuntar na da burin samar da kwambar jiragensa marasa matuƙa, waɗanda yake so, su riƙa sadarwa da juna tare da yin karakaina a sararin samaniya tsawon watanni idan sun tashi.

Facebook tun da farko ya bayyana gwajin jirgin na watan Yunin 2016 a matsayin wanda ya yi nasara, amma daga baya ya amsa cewa ya faɗo a lokacin sauka.

Ayarin jami’an da ke kula da harkokin jirgin sun ɗauki hoton bidiyon gwajinsa na biyu a lokacin da yake sauka inda suka buga a shafin intanet.

Aquila – wanda ke da faɗin fuka-fukan jirgin Boeing 737 – wani ɓangare ne na shirin Facebook don haɗa duniya da layin intanet.

A wannan mako, Facebook ya sanar cewa masu amfani da shafinsa sun kai mutum biliyan biyu, fiye da rubu’in yawan mutanen duniya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

699total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.