Jirgin Saman Ethiopian Zai Fara Jigila Daga Kaduna

Jirgin saman Ethiopian zai fara zirga zirga daga babban filin jirgin sama na jihar Kaduna zuwa sauran birane a fadin duniya nan. Gwamnan jihar ta Kaduna Mallam Nasir el-Rufa’i ya sanar da hakan ta shafin sa na Twitter a safiyar yau da misalin karfe 10:28.

A cewar Gwamnan na Kaduna, Ethiopian zai fara zirga zirga daga ranar 1 ga watan Agusta na 2017.

Masu sharhi a yanar gizo-gizo sun yaba da wannan yarjejeniya musamman ma ganin yadda Gwamna el-Rufa’i yayi namijin kokari wajen tabbatar da wannan yarjejeniya.

Jihar ta Kaduna zata shiga jerin birane hudu a Najeriya da jirgin saman Ethiopian yake tashi daga cikinsu.

646total visits,2visits today


Karanta:  An Yi Gangamin Ilimantar da Jama'a Kan Illar Ambaliyan Ruwa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.