John Heard: Jamurim Fim din Home Alone ya Mutu

Jarumi John Heard, wanda yayi fice a cikin fina nan Home Alone yana da shekaru saba’in da daya (71) a duniya.

An samu Heard a mace a cikin dakin sa na hotel a garin Palo Alto dake California kamar yadda jaridar TMZ ta wallafa a shashin ta na yanar gizo-gizo. Ya dai kasance yana zaune a wannan hotel din ne na akalla sati guda tun bayan wata ‘yar gajeriyar rashin lafiya da ya kamu da ita.

Heard ya fara shiga shirin fim ne a shekarar alif dari tara da saba’in (1970). Fina finan sa sun hada da Cutter’s Way, C.H.U.D da kuma Gladiator. An gabatar dashi a a shirin bayar da lambar girma da aka fi sani da Emmy Award a cikin shirin The Sopranos.

Asalin Labari:

Muryar Arewa da BBC Hausa

588total visits,1visits today


Karanta:  Musulman Rohingya na Fuskantar Wariya - Amnesty

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.