Kabilu Biyar Na Tsaunin Mambila Sun Yi Taron Hana Barkewar Rikici Tsakaninsu

A karkashin wata kungiyar wanzar da zaman lafiya, wasu kabilu biyar daga tsaunin Mambila sun yi taro a garin Gembu domin kawo zaman lafiya a yankin

Kabilun tsaunin Mambila biyar ne suka taru a filin wasan garin Gembu domin rigakafin hana sake barkewar duk wani rikici da sunan kabilanci ko addini ko kiyayyar manoma da makiyaya.

An gudanar da taron ne a karkashin wata kungiya mai wanzar da zaman lafiya.

Shugaban kwamitin karamar hukumar, Pastor Godwin Sawa ya ce fitinar da ta faru kwanakin baya inda aka samu hasarar rayuka da dauruwan shanu ba ta addini ba ce kuma an dauki duk matakan hana aukuwar irinta nan gaba.

Ya ce damuwar daya ce, ita ce damuwar manomi da makiyayi. Manomi yana son wurin noma haka ma makiyayi na bukatar wurin da zai yi kiwon dabbobinsa. Abun da ke hada fada ke nan.

Babban jami’in ‘yansanda na yankin Sardauna, Alabura Dangi, ya ce kabilun sun zama daya domin dukansu suna fulatanci.

A taron, Fulani makiyaya sun bukaci a hukumta baragurbin dake tsakaninsu da suke da hannu a kashe-kashen da suka gudana tare da biyan diya ga wadanda suka rasa shanunsu.

Shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya, Injiniya Zakari Ahmed Guroji, ya karfafa dawo da martabar sarakuna a matsayin wata hanyar hana irin fitinar da ta taso.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1308total visits,2visits today


Karanta:  Za a Kai Gwamnatin Taraba kotun ICC

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.