Kakakin Fadar Gwamnatin Najeriya Ya Bayyana Muhimancin Ziyartar Shugaba Buhari

A yayin da wasu kungiyoyin sa kai na Najeriya da ‘yan siyasa ke shirin zaman durshan cewar sai shugaba Muhammadu Buhari ya dawo akan karagar mulkinsa cikin kwanaki Talatin, kokuma su dukufa wajan fafutukar tsige shi daga kujerarsa ta shugaban kasa.

Wasu gwamnoni da shugabannin jam’iyyar APC sun ziyarci shugaban a birnin London.Shugabanin sun ziyaci shugaba Muhammadu Buhari a birnin London inda yake jiyya kuma sun yaba da koshin lafiyarsa tare da ba ‘yan Najeriya tabbacin dawowar shugaban nan ba da jimawa ba.

A kan wannan sanarwar da fadar gwamnatin Najeriyar ta bayar dangane da wannan ziyara yasa wakilin shasen Hausa na muryar Amurka, Umar Faruk Musa ya sami zantawa da Malam Garba Shehu, kakaki a fadar gwamnatin Najeriya, domin jin muhimmancin ziyarar.

Da yake bayani, kakakin fadar gwamnatin ya bayyana cewa daya daga cikin muhimmancin ziyarar shine kwantarwa da jama’a hankali musamman akan yadda ake ta cece kuce da kuma zancen daukar wasu mataka domin tsige shugaban.

Bayan hotunan da aka nuna na shugaban a shafukan yanar gizo, da alamu ‘yan Najeriya sun ganawa domin ganewa idanusu kasancewar yadda shugaban ya sami koshin lafiya.

Asalin Labari:

VOA Hausa

2682total visits,4visits today


Karanta:  Zamu Fadawa Buhari Damuwarmu Idan Yazo - Igbo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.