Kamaru: Wasu Dalibai Sun Kauracewa Komawa Karatu

Wasu 'yan kasar Kamaru daga yankin masu amfani da harshen Ingililishi, yayinda suke zanga-zangar neman gwamnati ta daina nuna musu wariya.

Akasarin Daliban makarantun dake kudu maso yammacin Kamaru masu amfani da harshen Ingilishi sun kauracewa komawa makaranta sakamakon bukatar fitowa zanga zanga da shugabannin yankin suka yi, kan yadda ake musguna musu.

Rahotanni sun ce an girke tarin ‘yan sanda cikin damara, domin kaucewa tada tarzoma a Buea, yayin da wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, yace kashi daya bisa 5 ne kawai na daliban makarantun suka koma karatu.

A makon jiya shugaba Paul Biya ya bada umurnin sakin shugabanin matasan da suka shirya zanga zangar a shekarar bara, wadda ta haifar da tahsin hankali.

Asalin Labari:

RFI Hausa

2239total visits,1visits today


Karanta:  Ana ruguguwar ficewa Florida kafin isowar guguwar Irma

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.