Kamfanin Alhazai Express Zai Fara Gudanar Da Koyar Da Na’urar Komfuta

Sanannen kamfanin yanar gizo gizo na Alhazai Express zai fara gudanar da tsarin koyar da komfuta kyauta.

Kamfanin Alhazai Express mai zaman kansa ya dauki alwashin fara gudanar da koyar da na’ura mai kwakwalwa a yankin arewancin Nigeria kyauta domin tallafawa matasa samun aikin yi cikin sauki. Sanarwar wanda shugaban kamfanin ya fitar ya nuna cewar nan bada dadewa ba kamfanin zai fara gudanar da kwas din a jihar Kano.

Zubairu Dalhatu Malami ya bayyana wa wakilin mu a jihar Kano cewar yin hakan zai bayar da dama ga samari musamman ma wadanda suka kammala karatun su na digiri samun damar dogaro da kai bayan kammala kwas din na sati uku.

Zubairu Dalhatu ya bayyana cewar bai kamata ace samari na dogara da gwamnati ba a yayin gama karatun su wajen samun aikin yi. Bugu da kari ya bayyana cewar kamfanin nasa zai zage dantse wajen tabbatar da cewar wadanda suka halarci kwasa kwasan sun amfana da tsarin kai tsaye inda zasu iya samun damar mallakar na’urar komfuta kyauta domin fara aiwatar da abubuwan da suka koya a lokutan yin kwas din. Daga karshe yayi kira ga gwamnatoci da su bayar da tasu gudummawar domin ganin cewar al’umma sun amfana da wannan tsari kai tsaye.

321total visits,2visits today


Karanta:  Kamfanin Facebook ya bijiro don yin gogayya da gidajen talbijin

Leave a Reply

Your email address will not be published.