Kano Ta Tantance Masu Girka Abinci 11,000 Don Shirin Ciyar Da Abinci A Makarantu

Yanzu haka an tantance masu girka abinci kusan 11,000 a Jihar Kano a shirye-shiryen da ake na fara ciyar da abinci a makarantu shirin nan na gwamnatin tarayya.

Hajiya Aishatu Jafar, Mai Taimakawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta Mussaman kan Shirin Tallafawa Al’umma ce ta sanar da haka a wata hira da sukayi da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ranar Asabar.

Jafar, wadda itace Babbar Jami’ar Gwamnatin Tarayya a Jihar Kano kan Shirin Tallafawa Al’umma tace an gudanar da tantancewar a wasu kebabbun cibiyoyin lafiya bakwai a jihar.

A cewar ta makasudin tantacewar shi ne a tabbatar da ingancin lafiyar su kansu masu girka abincin
“Muna bukatar masu kirka abinci sama da mutum 13,000 a Jihar Kano don gudanar da wannan shirin amma yanzu mutum 11,000 muka tantance.

“Kowacce mai girki bazata kirka abincin daliban da suka wuce 150 ba saboda samun girkawa yara ingantaccen abinci.

“Nan gaba kadan za a fara shirin a Jihar Kano saboda tuni aka kammala duk wasu shirye-shirye”, a cewarta.

A kan shirin nan na N-power kuwa, Jafar cewa tayi matasa 91,734 marasa aikinyi ne sukayi rijista a kaso na biyu na shirin a jihar a watan Yuli

Ta shawarci duk wadanda sukayi rijista da shirin dasu halarci tantan cewar da zayi nan gaba kadan

Ta yabawa Gwamnatin Tarayya bisa samar da shirin N-power wanda guda ne cikin shirye-shirye hudu karkashin shirin tallafawa al’umma.

Ta kara da cewa shirin tallafawa al’umma ya taimaka wajen kawar da muggan dabi’u a tsakanin matasa marasa abin yi a jihar dama kasa bakidaya.

Asalin Labari:

Daily Trust, Muryar Arewa

520total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.