Karbuwar Shugaba Donald Trump na Ta Sauka Zuwa Kashi 36%

Kano, Nigeria – Kaso 36% na Amurkawa ne kadai suka amince da jagorancin Shugaba Donald Trump a wata tantancewa da jaridar Washington Post tayi tare da hadin gwuiwar kamfanin dillancin labarai na ABC.

Wannan hakika ya baiwa Shugaba Trump mafi kankantar karbuwa a cikin al’umma a wata shida na farko a cikin shakaru saba’in na gwamnatin Amurka ga kowanne shugaban kasa a baya.

Karbuwar tasa tayi kasa ne daga kashi 42% na kwanaki 100 na farkon shugabancin sa. Haka zalika rashin amincewa dashi ya karu da kaso 5% izuwa kaso 58%.

A wata tantancewar kuma kaso 48% sunce hakika basu amince da tafiyar da mulkin sa ba.

Shugaba Trupm ya bayyana a shafin sa na Twitter cewar “Tantancewar ta kamfanin dillancin labarai na ABC da jaridar Washington Post, duk da haka kaso 40% ba laifi bane a wannan lokacin, kawai ya ta’alaka ne da rashin tabbataccen tantancewa a lokacin zabe!.

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa da CNN

3198total visits,1visits today


Karanta:  Amurka Tana Tunanin Ko Ta Dauki Matakin Soja Kan Venezuela

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.