Kasar Jamus Ta Tallafawa Kananan Hukumomi Hudu a Jamhuriyar Nijar

Kasar Jamus da wasu kasashen nahiyar turai sun tallafawa kananan hukumomi hudu a Jamhuriyar Nijar da zummar dakile kwararar matasa zuwa kasashen turai

Kananan hukumomi hudu na Junhuriyar Nijar ne kasar Jamus, a karkashin ma’aikatar harkokin wajen kasar, da wasu kasashen turai, suka tallafawa da zummar hana matasa yukurin ratsawa ta kasar Libya zuwa kasashen turai.

Mukhtari Usman, shugaban hukumar mashawarta ta jihar Damagaran, ya yi godiya tare da fatar tallafin zai taimaka wajen kawo ci gaban yankunan nasu.

Kayan da aka raba wa kananan hukumomin sun hada da mashina hudu, da kwamfutoci da wasu kayan aiki. Ana kyautata zaton kayan zasu taimaka wa matasan zama gida maimakon tafiya tafi cirani a wasu kasashen ketare.

Shima Sani Usman, Magajin Garin karamar hukumar Kurmi, daya daga cikin kananan hukumomin da suka ci gajiyar tallafin, yayi fatar tallafin zai taimaka wajen hana matasansu tafiya cirani.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1177total visits,1visits today


Karanta:  An Saki Tsohon Firaministan Libya Da Aka Sace

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.