Kiranye: Kotu Tayi Watsi Da Karar Da Sanata Melaye Ya Shigar

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja tayi watsi da karar da Sanata Dino Malaye ya shigar gabanta na kalubalantar shirin da Hukumar Zaben Kasar ke kokarin  aiwatarwa kan shirin yi masa kiranye.

Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ranar litinin ya zartar da hukuncin cewa duk korafe-korafen da Melaye yayi basu cancanta ba haka kuma yakamata ayi watsi dasu.

Kan korafin da ya shigar cewa akwai rashin adalci gurin jin ta bakin wadanada yake wakiltar kafin a mika korafin kiranyen zuwa Hukumar Zaben, Mai shari’a yace wannan ba dalili bane don haka yayi watsi da korafin.

Mai Shari’a Dimgba ya zartar da hukuncin cewa abun da ya shafi kiranye magana ce ta siyasa don haka bata cikin hurumin kotu.

Yace ba alhakin wadanda Malayen yake wakilta bane su mika masa kofin korafin kiranyen.

Ya kara da cewa Malaye nada damar yin kamfen ga masu zabe kafin gudanar da zaben raba gardama don bayyana musu nasarorinsa kamar yadda jadawalin kwanaki 90 ya nuna da kuma tsare-tsaren da Hukumar Zaben ta tsara aiwatarwa kamar yadda sashi na 69 na kundin tsarin mulki ya bayyana.

“Jama’ ne suka zabe shi a ofis, suka bashi ofis din kyauta, don haka suna da damar karbe kyautar da suka bashi,” a cewarsa.

Don haka Alkalin ya kori korafin na Melaye na cewa korafe-korafen da aka shigar na yi masa kiranyen shifcin gizo ne wadanda aka samu daga gurin marasa gaskiya don haka babu adalci a cikinsu.

Ya kuma yi watsi da zargin da Sanatan yayi cewa mutanen 188,000 da suka sakawa takardar korafin hannu ta kunshi mutanen da bana gaskiya ba, da matattu dama na bogi, yana mai cewa yayi gaggawar shigar da wannan korafin tunda bai gama bin gabadayan shirin tantance sa hannun na hukumar zaben ba
Alkalin ya bayyana korafin Melayen na cewa ya kamata a bawa ma’aikatan zaben takardun rantsuwa don nuna cewa su ‘yan ba ruwanmu ne da cewa yayi “gaggawa” don ba a gama tabbatarwa cewa za a gudanar da zaben kiranyen ba

Karanta:  An Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Legas

Alkalin ya kuma ummarci Hukumar Zaben data bawa Melaye takardar kiranyen, da takardun da jama’a suka sakawa hannu na kiranyen dama cikakken sunayen duk wadanda suke goyon bayan kirayen kamar dai yadda suke kunshe kafin a fara gudanar da tantancewar.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

857total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.