Ko Kunsan Kasar Da Ake Damawa Da Mata A Wasan Tamola?

Bisa al'ada wasan kwallon kafa an fi alakanta shi da Maza, amma yanzu mata sun fara nuna sha'awar wannan fanni a Afirka.

Kamar a kasar Ghana, wasu matasa mata sun yunkuro don shiga a dama da su a fagen wasan kwallon kafa.

Sai dai kuma lamarin ka iya fuskantar cikas ta fuskar Addini da al’ada.

To amma wasu matan da suka fito daga arewacin kasar ta Ghana, sun toshe kunnensu tare da fara atisaye don ganin burinsu ya cika.

Wata matashiya da take buga wasan kwallon kafar a kasar, ta shaida wa BBC cewa, wasu iyayen basa barin ‘ya’yansu mata su shiga kungiyar wasan kwallon kafa, saboda canfawar da aka yi cewa mace ba za ta haihu ba idan tana buga wasan kwallon kafar.

Ta ce wannan dalili ne ke sa wasu matan fita daga kungiyoyin wasan kwallon kafar duk da sha’awar da suke da ita ta wasan.

A Arewacin kasar Ghana kadai, akwai kungiyoyin wasan kwallon kafa na mata guda 12 da suke yin wata gasa domin samun damar wakiltar kasar a wasannin Premier League.

Wasu a kasar dai na ganin cewa bai kamata a bar mata su rinka sanya suturar da zata rinka nuna tsiraicinsu ba, kuma kayan da matan kan sanya idan za su buga wasan kwallon kafar sam ba su dace da suturar da musulunci ya yarda da ita ba

Asalin Labari:

BBC Hausa

3895total visits,4visits today


Karanta:  An yi hatsaniya tsakanin magoya bayan Buhari da masu son ya sauka

Leave a Reply

Your email address will not be published.