Komitin Sulhu na MDD Zai Dauki Mataki Kan Korea ta Arewa Littini

Littinin nan ne Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke zama na musamman domin tattauna batun sake gwajin makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi, don duba irin matakin da ya dace a dauka.

Kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Japan da Korea ta Kudu suka bukaci zaman na musamman  na littini.

Tun jiya lahadi Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da ayarin mashawartansa game da harkokin tsaro inda suka duba gwaji na baya-bayan nan na makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi.

Sakataren Watsa labarai na Ofisshin Shugaban Amurkan Sarah Huckabee Sanders na cewa ayarin jami’an tsaron  Amurka na bin dukka abubuwan dake gudana cikin hankali.

Shugaban Gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron sun nemi lallai kungiyar Tarayyar Turai  ta kara kakabawa Korea ta Arewa takunkumi sakamakon sake gwajin makami mai linzami da ta yi.

Asalin Labari:

RFI Hausa

399total visits,1visits today


Karanta:  Korea Ta Arewa Ta Yi Sabon Gwajin Makami

Leave a Reply

Your email address will not be published.