Korea Ta Arewa na tallafa wa ta’addanci- Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Korea Ta Arewa a matsayin kasar da ke tallafa wa ayyukan ta’addanci, abin da ya maido da kasar cikin jerin sunayen makiyan Amurka.

A lokacin da ya ke ayyana Korea Ta Arewa a matsayin kasa mai tallafa wa ta’addanci a fadar White House, Trump ya ce, tun da jimawa ya kamata su dauki wannan mataki.

Korea Ta Arewa na ci gaba da kasancewa cikin jerin takunkuman da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka kakaba ma ta saboda gwaje-gwajenta na makamin nukiliya.

Sai dai ana ganin sabon matakin na Amurka ba zai yi gagawaan tasiri ba wajen gurgunta tattalin arzikin kasar.

A shekarar 2008 ne tsohon shugaban Amurka George W. Bush ya janye Korea ta Arewa daga jerin makiyan kasar, yayin da ake kallon maido da ita a matsayin yunkurin kara matsin lamba a kan gwamnatin Kim Jong-Un .

Trump ya ce, baya ga barazanar makamin nukiliya da Korea Ta Arewa ke yi wa duniya, kasar na ci gaba da tallafa wa ayyukan ta’andanci da suka hada da kashe-kashe a kasashen ketare.

A bangare guda, Korea ta Kudu ta ce, makwabciyarta Korea Ta Arewa na shirin sake cilla makaman nukiliya a cikin wannan shekara don zafafa barazanarta ga Amurka.

Asalin Labari:

RFI Hausa

621total visits,1visits today


Karanta:  Amurka ta Sanyawa Kamfanonin Rasha da Chana Takunkumi

Leave a Reply

Your email address will not be published.