Kotu ta wanke Saraki kan kin bayyana kadarorinsa

Kotun kula da da’ar ma’aikata ta Najeriya ta yi watsi da karar da ke gabanta wadda ake tuhumar shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki da laifin kin bayyana kadarorinsa.

A lokacin da yake yanke hukunci, Babban alkalin kotun daukaka karar Danladi Umar, ya ce masu shigar da karar sun gaza gabatar da kwararan hujjoji kan zarge-zargen da ake masa.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Laraba da safe.

Me yasa kotun ta wanke Sanata Saraki?

An wanke shi ne saboda kotun ta ce babu wata hujja da gwamnatin tarayya, wacce ita ce ta shigar da karar, ta gabatar da zai sa a ci gaba da tuhumar Sanata Sarakin.

Alkali Danladi Umar ya ce shaidun da masu shigar da karar suka gabatar sun bayar da hujjoji masu karo da juna wadanda ba za a iya amfani da su wajen yanke masa hukunci ba.

Alkalin ya kara da cewa rahoton da hukumar EFCC ta gabatarwa kotun ya fi kama da bayanan da aka samu ta hanyar samun bayanan sirri maimakon ainihin bincike na shari’a.

Sai lauyoyi sun yi musu bayani kan abin da ya wakana kafin su yi martani akai.

Dama dai ana tuhumar Sanata Sarakin ne da laifuka 18 a karar da hukumar EFCC ta shigar.

Tun a watan Satumbar 2015 ne aka fara tuhumar Sanata Saraki da laifukan da suka danganci cin hanci da rashawa da kuma kin bayyana kadarorin da ya mallaka, a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara.

Kazalika, ana kuma zarginsa da mallakar kadarorin da suka fi karfin aljihunsa da mallakar asusun ajiyar kudade a kasashen waje a lokacin da yake rike da mukaman gwamna da kuma a matsayin sanata.

Karanta:  Kotu Ta Mallakawa Gwamnatin Najeriya Wasu Gidajen Mrs Madueke dake Legas
Asalin Labari:

BBC Hausa

370total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.