Kotu Taci Tarar Patience Jonathan Naira Dubu Dari Biyar

Alkali Saliu Seidu na wata babbar kotu dake zaman ta a garin Fatakwal na jihar Rivers a Najeriya ta kallafawa uwar gidan tsohon shugaban Nigeria Dakta Patience Jonathan tarar kudi Naira Dubu Dari Biyar sakamakon janye karar da ta shigar a gaban ta kan hukumar yaki da cin hanci a Najeriya wato EFCC.

Ita dai uwar gidan Jonathan ta shigar da karar ne a watan Fabrairu na 2017 inda take neman a kotun na bata dama a matsayin ta ta ‘yar kasa domin mallakar kadarori, ‘yancin sauraro da dai sauran koke koke.

Bayan janye karar da tayi lauyan EFCC ya nemi kotu da ta tilastawa Dr. Patience da biyan kudi da suka kai N500,000 domin samun mayar da asarar da sukayi domin neman kare kansu.

Daga bisani alkalin ya kori karar.

355total visits,2visits today


Karanta:  Kotu ta mallakawa gwamnati kadarorin Diezani

Leave a Reply

Your email address will not be published.