Kotun Kolin Iraqi Ta Dakatar Da Zaben Raba Gardamar Yankin Kurdawa

Kotun kolin kasar Iraki ta bada umarnin soke gudanar da zaben raba gardamar da yankin kudrustan ya shirya gudanarwa a ranar 25 ga wannan wata na Satumba, har sai ta kammala sauraren kararakin da aka gabatar mata akan zaben, kamar yadda ta sanar a cikin wata sanarwa a yau litanin.

Ofishin Firaministan Iraki ya bayyana cewa Haidar Al-Abadi ne ya shigar da karar da ke kalubalantar duk wani shirin da zai kai ga ballewar ko wane irin yanki na kasar ta Iraki tare da bukatar ganin kotun ta soke gudanar da zaben.

A cewar majiyoyi a majalisar dokokin kasar, a kalla yan majalisar dokoki yan shiá da turkawa 8 ne, da ke zama tsirari a yankin da ake jayayya a kansa na Kirkouk, a arewacin Bagdad ne suka shigar da bukatar ganin kotun ta hana gudanar da zaben raba gardamar.

Kasashe makwabta da Amruka da sauran masu korafi kan yankin da ke cin moriyar kwaryakwaryar yancin cin gashin kai tun cikin shekarar 1991, na fatan ganin yankin ya magance sabanin da ke tsakaninsa da mmahukuntan Bagdad, ba tare da ta kai shi ga ballewa daga kasar da yanzu haka mayakan jihadi ke ci gaba da jan daga a wasu tingaye biyu da suke rike da su ba.

Shugaban yankin kurdawan Massoud Barzani ya ce, tattaunawa da Bagdad ba zai haifar da samar masu kafa kasa mai cin gashin kai cikin hanzari ba, lura da yadda a farkon tattaunawar magance barakar da ke tsakaninsu akan cimma turjiya.

502total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.