Kundin Tsarin Mulki: Dan Shekara 35 Zai Iya Tsayawa Shugaban Kasa

Shugaban Majalisar Wakilai ta Kasa Yakubu Dogara

A kokarin sauya kundin tsarin mulkin Najeriya Majalisar Walikai ta Kasa tayi yunkurin rage shekarun dan takarar shugaban kasa izuwa talatin da biya (35 years) a wani kuduri na gyara da za’ayi anan gaba.

Haka zalika ta yi yunkurin gyara wadan su bangarori da suka hada da:

  • Babu shiga zaben zagaye na biyu ga mataimakin shugaban kasa ko gwamna wanda ya gaji shugaba a yanayi na mutuwa.
  • ‘Yan Najeriya zasu iya tsayawa takara a kashin kansu ba tare da jam’iyya ba.
  • Kananan hukumomi zasu ci gashin kansu.
  • kaso talatin da biyar (35%) na mukamai zai tafi ga mata zalla.

Zabe a nan gaba a Najeriya zai zama ga kowanne dan Najeriya da shekarun sa suka kai talatin da biyar (35 years) zuwa sama idan har aka amince da gyaran tsarin mulkin dake gaban majalisar a yanzu.

A halin yanzu shekarun takara a Najeriya ga ‘yan kasa ya kama daga shekara arba’in (40 years).

Bugu da kari, ‘yan Nijeriya masu sha’awar takarar majalisun dokoki na jiha da kuma wakilai na tarayya zasu iya tsayawa daga shekaru 25 (25 years) wanda a baya yake shekara 30.

774total visits,2visits today


Karanta:  'Yan majalisar Nigeria sun sayi motocin 'kece-raini' 200

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.