Kungiyar Malaman jami’a tace Sojoji Sun Shara Karya.

Malaman jamiaar Maiduguri sunce jamiaan tsaro sun shara karya domin sun sanar da duniya cewa sun kwato mutanen da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa dasu ashe matattu suka kwato.

 

Kungiyar Malamai jami’a reshen Maiduguri sun bayyana alhinin su game da rasuwar wasu abokan aikin su da aka kashe sakamakon kwanton bauna da ‘yan kungiyar Boko Haram tayi musu.

Da yake Magana da wakilin Sashen Hausa, Haruna Dauda Biu, shugaban kungiyar Malaman Dr. Daniel Mamman yace yana mika taaziyar kungiyar ga iyaye da ‘yan uwan wadanda wannan lamari ya rutsa dasu.

Yace wannan abu da ya faru basu kadai ne zasu ji da wannan bakin cikin ba, har da suma abokan aikin su.

Dr Daniel yace fatar su ita ce su wadanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba,ALLAH ya bayyanar dasu kuma cikin koshin lafiya.

Su kuma wadanda suka riga mu ALLAH ya jikan su.

Asalin Labari:

VOA Hausa

696total visits,3visits today


Karanta:  Malaman Nigeria na adawa da 'yancin kananan hukumomi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.