‘kwalara ta yi sanadin mutuwar mutum 1,500 a Yemen’

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da sanarwar cewa mutum 1,500 ne a yanzu suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa a Yemen.

Ƙasar dai a yanzu tana fuskantar ɓullar cutar amai da gudawa ko kwalara mafi muni a duniya.

Cutar wadda ke yaɗuwa ta hanyar ruwa na bazuwa cikin hanzari a faɗin Yemen tun cikin watan Afrilu.

Jakadan Hukumar Lafiya a Yemen, Nevio Zagaria ya faɗa wa wani taron manema labarai a Sana’a babban birnin ƙasar cewa kusan mutum dubu 250 ne ake zargin suna fama da cutar a Yemen.

Rubu’in mutanen da aka ba da rahoton sun mutu sakamakon cutar ƙananan yara ne.

Cutar amai da gudawa wadda ta fi tasiri a wuraren da ƙazanta ta yi sansani ta auka wa Yemen, yayin da ake ci gaba da tafka faɗa tsakanin ƙawancen dakaru ƙarƙashin jagorancin Saudiyya da kuma ‘yan tawayen Houthi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

462total visits,2visits today


Karanta:  Likitoci Na Cigaba da Yajin Aiki a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.