Kwankwasiyya Tayi Barazanar Zuwa Kotu Sakamakon Fadan Da Ya Faru A Kano Da Gandujiyya

A kalla mutane 20 ‘Yan Darikar Kwankwasiyya aka tabbatar an jiwa rauni bayan barkewar fada tsakanin masoyan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da masoyan wanda ya gada a mulki Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.

Magoya bayan ‘yan siyasar biyu sun gwabza fada a harabar fadar mai martaba yayin Hauwan Dushe ranar  Asabar.

Yayin da yake tabbatar da adadin wadanda abin ya rutsa dasu a wani taron manema labarai tsohon Kwamishina a karkashin mulki Kwankwaso, Dr Yunusa Adamu Dangwani cewa yayi zasu dauki matakin shari’a kan wadanda suka shirya musu hakan.

“Zamu je Kotu da zarar mun gama kamalla bayanan mu. Abin takaici ne ace wasu mutane a cikin gwamnati su jagoranci ‘yan daba su kaiwa mutanen da basa dauke da makami farmaki. Ba zamu bari hakan ta cigaba da faruwa ba muna kallo,” a cewarsa.

“Tuni muka gane wasu daga cikin mutanen da suka yiwo hayar ‘yan daban. Mun gane jami’an gwamnati uku ciki harda Dan Majalisar Jiha wanda ya jagoranci ‘yan daban kai mana farmaki. Sun jikkata mutum 20 mambobin darikar Kwankwasiyya a lokacin da aka kawo farmakin.”

Ya nuna takaicinsa da gwamnatin da Gandujen ke jagoranta inda take son zama wani abu daban, yake cewa “Bamu zabi wannan gwamnatin ba don ta kaishe mu. Gwamnatin na amfanin da kudaden al’umma tana hayar ‘yan daba su kaiwa mutanen da basu jiba basu gani ba hari.”

Tsohon kwamishinan yayi kira ga mambobin darikar Kwankwasiyyar da kada su dauki doka a hannunsu, inda yake tabbatar musu cewa zasuyi duk wani abun da suke da iko don tabbatar cewa an hukunta wadanda suka shirya wannan lamari kamar yadda doka ta tanada.

Karanta:  Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Buhari a London

Koda yake tuni Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Muhammad Garba yayi watsi da zargin da akeyi cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya dauki nauyin kai farmakin.

Garba yace ba hannun gwamna ko hannun wani jami’in gwanati a kai farmakin

Kwamishinan yace zargin da Kwankwasiyyar ke yiwa gwamna da gwamnati bashi da tushe ballantana makama, ya kara da cewa gwamnati na iya kokarinta na gani an sami zaman lafiya a jihar.

Yace, “Ya za ace gwamnatin da take kokarin wanzar da zaman lafiya a lokaci guda kuma ita ce zata shirya hari akan jama’arta. Wannan zargi ne da bashi da tushe wanda duk wani mai hankali ba zai dauka ba.”

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1599total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.