Likitoci Na Cigaba da Yajin Aiki a Najeriya

Rahotanni daga Ibadan babban birnin jihar Oyo na nuni da cewa likitocin asibitin koyaswa ko UCH, asibitin koyaswa na farko a duk fadin kasar na cigaba da yajin aiki

Yau likitocin da ake kira Resident Doctors suka shiga rana ta biyu na yajin aikin da suka soma yi a duk fadin kasar.

A asibitin koyaswa dake Ibadan babban birnin jihar Oyo, wato UCH, likitocin wurin na cigaba da yajin aiki kamar sauran ‘yanuwansu a kasar.

Shugaban kungiyar likitocin masu neman kwarewa a fannoni daban daban na kiwon lafiya ko Resident Doctors, Dr. Olusegun Olofa ya tabbatar cewa suna yajin aiki ne saboda gwamnati ta ki aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla tun shekarar 2013 har zuwa yau.

A cewarsa a watan Yuli sun ba gwamnati sanarwar zuwa yajin aiki idan ba’a biya masu bukatunsu ba a karshen kwanaki 21 daga ranar sanarwar. Da lokaci ya kure sun kara bada kwanaki bakwai amma shiru ka ke ji kamar an shuka dusa. Inji shugaban sai ranar da suka fara yajin aiki ne gwamnati ta waiwayesu.

Likitocin na neman gwamnati ta biyasu cikakken albashi kamar sauran ma’aikatan kiwon lafiya a asibitoci da gwamnatin take biya..

Asalin Labari:

VOA Hausa

977total visits,2visits today


Karanta:  Kashe Nnamdi Kanu sojin Nigeria suka zo yi - Bar Ejiofor

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.