Lionel Messi ya yi aure da rabin ransa tun suna yara

An ɗaura auren tauraron ƙwallon ƙafa Lionel Messi da rabin ransa tun suna yarinta, Antonela Roccuzzo a garinsu Rosario cikin Argentina ranar Juma’a.

Dan wasan na Barcelonan ya koma mahaifarsa Rosario domin shagalin aurensa da Antonella Roccuzzo, wadda suke tare kafin ya koma Spaniya a lokacin da yake dan shekara 13.

Jaridar Argentina Clarín ta bayyana auren a matsayin “auren da ya fi kowanne a wannan shekara” da kuma “auren da ya fi kowanne a wannan ƙarnin”.

Baki 260 ne suka halarci shagalin bikin, ciki har da takwarorin Messi a taka leda Luis Suárez da Neymar.

Yawancin bakin sun isa da jiragensu.

An kara yawan ‘yan sanda domin a tabbatar da tsaro a harabar otel din za a yi auren, yayin da wani kamfani tsaro mai zaman kansa zai yi aiki ciikin otel din domin hana wadanda ba gayyata ba shiga.

An yi wa kimanin ‘yan jarida 150 rijistar shiga wani wurin manema labarai na musamman, amman ba za su samu cikakkiyar daman shiga wurin da za a cashe bikin ba, in ji masu shirya taron.

A ina amarya da ango suka hadu?

Messi, mai shekara 30, ya hadu da amaryarsa ne a lokacin da yake dan shekara biyar.

‘Yar uwa ce ga babban abokinsa, Lucas Scaglia, wanda shi ma ya zama dan wasan kwallon kafa.

Messi ya yarda da yarjejeniyar taka wa Barcelona leda ne a lokacin yana dan shekara 13, bisa sharadin cewar kungiyar za ta dauki nauyin nema masa maganin wata cuta.

Ya yi bayani kan irin kalubalen da ya fuskanta na barin abokan arzikinsa a baya da kuma tsohuwar kungiyarsa ta kwallon kafa.

Karanta:  Willy Caballero: Chelsea ta sayi tsohon mai tsaron gidan Manchester City

Ango Messi da amaryarsa, wadanda suke zaune a yanzu a birnin Barcelona, suna da yara maza biyu.

A watan Mayu, an yi watsi da daukaka karar da ya yi kan hukuncin daurin wata 21 da aka yi masa sakamakon kin biyan haraji a Spaniya.

Zai yi wuya ya shiga kurkuku domin za a iya hukunta shi ta wa’adin gyara hali ko kuma biyan tara.

Me muka sani game da babbar ranar?

Za a yi bikin ne a otel din City Center da ke garin Rosario, wanda yake da gidan caca a gefensa.

Su wane ne kan jerin sunayen baki?

Rahotanni sun ce Messi ya gayyaci tawagar ‘yan wasan Barcelona, ciki har da Gerald Piqué da kuma matarsa, taurariyar waka Shakira.

Takwarorinsa na tawagar wasan kwallon kafa na Ajentina, ciki har da Sergio Agüero, za su kasance a taron.

Clarín ta ruwaito cewar bai gayyaci kowa daga cikin koca-kocansa na baya-bayanan ba, har da kocin Mancester City na yanzu, Pep Guardiola.

Rahotanni daga kasar sun ce gwarzon dan wasan Ajentina Diego Maradona yana cikin wadanda za su halarci bikin.

A ina Rosario ya ke?

Birni mai tashar jirgin ruwa na Rosario yana gabar kogin Paraná, kimanin kilomita 300 arewa maso yammacin Buenos Aires a tsakiyar kasar .

Wani shararren dan Ajentina da ya fara rayuwarsa a wannan wuri shi ne Ernesto “Che” Guevara.

An fi sanin Messi da suna Lío a wannan wuri.

Tun da ya koma Spaniya, Messi ya lashe kyautar Fifa ta Ballon d’Or guda biyar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

819total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.